10 Afirilu 2026 - 14:35
Source: ABNA24
Jagora: Al’umma Su Ci Gaba Da Halartar Fagagenen Gwagwarmaya

Jagora ga al’ummar Iran: “Yan’uwa maza da mata na ƙasarmu, a yau—har zuwa wannan mataki na jarumtakar “Kariya mai Tsarki na Uku”—za a iya faɗa da ƙarfin gwiwa cewa ku, jarumar al’ummar Iran, kun riga kun zama masu nasara a wannan fage.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) nakaltowa daga Kamfanin Dillancin Labaran Hauza: cewa sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei ya fito ne a ranar cika kwanaki arba'in da shahadar babban jagoran juyin juya halin Musulunci (Allah ya tsarkake ruhinsa), tare da batutuwa masu muhimmanci da suka shafi Kallafaffen Yaƙi na Uku.

Ga Fassarar Cikakken Sakon:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

“Lallai Mun ba ka nasara mabayyaniya, domin Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata na laifinka da abin da zai zo daga baya, Ya cika ni’imarsa a gare ka, Ya shiryar da kai zuwa hanya madaidaiciya, kuma Ya taimake ka da taimako mai ƙarfi.”

Yanzu kwanaki arba’in sun wuce tun bayan daya daga cikin manyan laifuffukan da makiyan Musulunci da Iran suka aikata, da kuma daya daga cikin manyan bakin cikin da wannan al’umma ta taba fuskanta a tarihinta: wato shahadar babban jagoran juyin juya halin Musulunci, uban al’ummar Iran, jagoran al’ummar Musulmi, kuma jagoran masu neman gaskiya a wannan zamani, wato Shugaban Shahidan Iran da ƙungiyoyin gwagwarmayar – Khamenei mai girma, Allah Ya tsarkake ruhinsa.

Kwana arba’in kenan ruhin wannan jagora shahidi yake cikin kusanci da Allah yana tare da waliyyai, siddiqai da shahidai. A lokaci guda kuma, ko bayan haka, mutane da dama daga cikin abokan tafiyarsa, kwamandojin yaki, mayaƙan Musulunci da kuma fararen hula marasa laifi – daga jarirai ƙanana har zuwa tsofaffi – sun samu wannan babban daraja ta shahada.

Kwana arba’in da darare kenan Allah Madaukaki Ya kira jagoran wannan al’umma zuwa gare Shi. Amma wannan karon, sabanin abin da ya faru a zamanin Annabi Musa (AS), mabiyan jagoran shahidi da al’ummarsa sun tashi domin tsayawa tsayin daka wajen kafa gaskiya da yakar ƙarya. Sun tsaya kamar duwatsu masu ƙarfi a gaban Samiri da gunkinsa, kuma kamar lava mai zafi sun sauka a kan masu zalunci da masu girman kai.

Tsawon kwanaki arba’in, manyan masu girman kai na duniya sun cire abin rufe fuskokinsu na yaudara da ƙarya, suka nuna a fili mummunar fuskar kisa, zalunci, hari, ƙarya, girman kai, kashe yara, danniya da fasadi.

Amma a gefe guda kuma, tsawon kwanaki arba’in, ‘ya’yan Imam Khumaini da shahidi Khamenei da mabiyan Musulunci na gaskiya sun nuna jarumta ta musamman. Sun kasance a filaye, tituna da wuraren yaki. Duk da irin barnar da makiya suka yi, sun maida wannan Kallafaffen Yaƙi na Uku yaki ya zama wani sabon labari na jarumtaka kamar yadda aka gani a lokacin “Kariya mai Tsarki” (Difa'e Muƙaddas) na baya.

Al’ummar Iran masu wayo sun nuna cewa ko da suna cikin bakin cikin rasa jagoransu, sun maida wannan bakin ciki ya zama jarumtaka, kamar yadda magada na gaskiya na Karbala suka yi. Wannan ya ba makiya mamaki kuma ya sa masu neman ‘yanci a duniya suna yaba musu.

Wannan jahilci da kuskuren makiya ya sa watan Esfand na shekara ta 1404 (Maris, 2026) ya zama farkon sabon zamani na ƙarfafa Iran da juyin juya halin Musulunci, inda tutar Iran ba kawai a cikin iyakokin kasar ba, har ma a cikin zukatan masu neman gaskiya a duniya ta filfila.

Siffofi Da Basirar Shahidin Jagora

Wannan lokaci ya ba da dama mu yi dan taƙaitaccen bayani game da wannan babban jagora. Mutum ne da ya shahara sosai, amma ba a san shi yadda ya kamata ba. Kowa ya san cewa jagoranmu shahidi ya kasance malami mai zurfin fahimta, mai hangen nesa, jarumin da ba ya gajiya, mutum mai ƙarfi kamar dutse, malami mai aiki da iliminsa, mai ibada, mai yawan zikiri da addu’a, kuma mai tsananin tawakkali ga Allah.

Daga cikin siffofinsa akwai ƙaunar Iran da kuma ƙoƙarin tabbatar da cikakken ‘yancin kai na ƙasar. A lokaci guda yana jaddada haɗin kai na ƙasa. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina tsarin Musulunci da tabbatar da ci gaba da wanzuwarsa, kuma a gare shi, Jamhuriyar Musulunci ba ta da ma’ana idan ba tare da jama’a ba.

Duk da ƙarfinsa da tsaurinsa a matsayi na jagora, yana da laushi da hikima a tunani da tafiyar da al’amura. Yana ba matasa muhimmanci sosai, yana kuma ƙarfafa ilimi da fasaha domin ci gaban ƙasa. Yana girmama iyalan shahidai, waɗanda suka ji rauni saboda yaki, da sauran jarumai.

Daya daga cikin manyan basirorinsa shi ne iya gina al’umma ta hanyar tsara tunanin jama’a da ruhin su. Haka kuma yana da basirar kafa cibiyoyi da tsare-tsare masu hangen nesa tun farkon jagorancinsa.

Wani muhimmin abu shi ne ƙarfafa tsarin tsaron ƙasar, wanda al’ummar Iran suka amfana da shi a  Kallafaffun yaƙe-yaƙe na baya-bayan nan. Haka kuma yana da basirar kirkira a fannoni daban-daban na ilimi, dabaru da manufofi.

Daga cikin halayensa shi ne akwai hangen nesa mai zurfi wajen hasashen abubuwan da za su faru a nan gaba, kamar yadda ake cewa: “Mumini yana gani da hasken Allah.”

Duk waɗannan baiwar Allah ne na musamman da kuma albarkar Ahlul-Baiti. Amma wani muhimmin darasi daga rayuwarsa shi ne sadaukarwa da taimakon juna da kuma tausayi tsakanin mutane.

Idan mutane suka rungumi wannan hali, to kofofin rahamar Allah za su buɗe, kuma taimakon Allah zai sauko – daga saukar ruwan sama na rahama har zuwa nasara a kan makiya da kuma ci gaban ilimi da fasaha.

A cikin waɗannan kwanaki ana yawan jin yadda ƙungiyoyi daban‑daban na jama’a masu daraja, cikin gaskiya da kewar wancan lokaci na musamman, suke tunawa da shi. A hankali kuma ana ƙara gano wasu fannoni na hasken halayen wannan babban mutum. Haka kuma ana ganin mutane suna ƙara ƙoƙarin yin koyi da wasu ayyukansa. Misali, jama’armu sun koyi darasi daga yadda ya matse hannunsa ya zama ƙulli a lokacin shahadarsa, kuma yanzu wannan hannu mai ƙulli ya zama wani irin alama ta haɗin kai da akida ga wasu. Wannan yana sake tabbatar da cewa tasirin shahidi ya fi na wanda yake raye; muryarsa wajen kira zuwa tauhidi, neman gaskiya da yaƙi da zalunci da fasadi ta fi ƙarfi bayan shahadarsa fiye da lokacin rayuwarsa. Haka kuma burin zuciyar wannan babban shahidi—wato farin ciki da ci gaban wannan al’umma da sauran al’ummomin Musulmi—yana ƙara kusantar zama gaskiya.

Nasarar Jarumar Al’ummar Iran A Kallafaffen Yaƙi Na Uku

“Yan’uwa maza da mata na ƙasarmu, a yau—har zuwa wannan mataki na jarumtakar “Kariya mai Tsarki na Uku”—za a iya faɗa da ƙarfin gwiwa cewa ku, jarumar al’ummar Iran, kun riga kun zama masu nasara a wannan fage.

Yanzu an fara ganin hasken bayyanar Jamhuriyar Musulunci a matsayin babban ƙarfi, yayin da girman kai na masu iko a duniya ke gangarowa zuwa rauni a gaban idon kowa. Ba shakka wannan ni’ima ce ta Allah, wadda ta zo ne sakamakon jinin jagoranmu shahidi da sauran shahidai masu girma, da kuma shahadar jama’a marasa laifi da yara da aka kashe a makarantar Shajarat Tayyiba ta Minab. Haka kuma ta zo ne sakamakon addu’o’i da kuka na al’ummar ƙasa ga Allah, da kuma halartar su da jajircewa a filaye, unguwanni da masallatai, da sadaukarwar mayaƙan Musulunci a cikin Sepah, sojoji, Faraja (ƴan sanda), jami’an tsaro na sirri da masu tsaron kan iyaka.

Wannan ni’ima kamar kowace ni’ima dole ne a yi mata godiya domin ta dore kuma ta ƙaru. Allah Ya ce: “Idan kuka yi godiya, zan ƙara muku.” Godiya a aikace ga wannan ni’ima ita ce yin aiki ba tare da gajiyawa ba domin cimma burin Iran mai ƙarfi.

Muhimmancin Ci Gaba Da Kasancewar Jama’a A Sahu

Abin da ya zama wajibi a wannan lokaci domin cimma wannan babban buri na jagoranmu shahidi shi ne ci gaba da kasancewar jama’a a fagen gwagwarmaya kamar yadda suka yi a kwanaki arba’in da suka gabata. Wannan kasancewa muhimmin ginshiƙi ne na matsayin da Iran mai ƙarfi ta kai a yau.

Saboda haka bai kamata a ɗauka cewa idan an sanar da yiwuwar tattaunawa da maƙiyi to ba a buƙatar jama’a su kasance a tituna ba. Ko da kuwa an shiga wani lokaci na shiru a fagen yaƙin soja, nauyin da ke kan jama’ar da za su iya halartar filaye, unguwanni da masallatai ya fi na baya nauyi.

Tabbas shelanta sautunku a fagage yana da tasiri a sakamakon tattaunawar, kamar yadda yawan mutane masu shiga cikin kamfen “Sadaukar da Rai domin Iran” da ke ƙaruwa zuwa miliyoyi shima yana da tasiri a wannan fage. Da izinin Allah, sakamakon wannan ci gaba da rawar da jama’a ke takawa, makomar da ke gaban al’ummar Iran ita ce wani zamani mai ɗaukaka, cike da girma, mutunci da wadata.

Lokacin da jagoranmu shahidi ya karɓi jagoranci, tsarin Jamhuriyar Musulunci kamar wata ƙaramar shuka ce da ta sha raunuka daga makiyan Iran da Musulunci, amma ta jure. Bayan kusan shekaru 37 na jagorancinsa, ya bar wata bishiya mai albarka mai ƙarfi wadda tushenta ya yi ƙarfi kuma rassanta sun bazu a sassa masu muhimmanci na yankin da ma duniya.

Hanyar kaiwa ga Iran mafi ƙarfi tana wucewa ta hanyar haɗin kai tsakanin sassa daban‑daban na al’umma, abin da shi ya jaddada sau da yawa. A cikin waɗannan kwanaki arba’in an ga wani ɓangare mai muhimmanci na wannan haɗin kai: zukata sun kusanto, bambance‑bambancen da ke tsakanin jama’a sun fara narkewa, kuma kowa ya taru ƙarƙashin tutar ƙasa.

Yanzu mutane da dama suna kallon makomar al’umma da hangen nesa na wayewa da ci gaban al’umma. Wannan halayya a baya tana cikin mutane kaɗan ne kawai, tare da jagoran shahidi a gaba. Saboda haka duk wanda ya lura yana ganin saurin ci gaban wannan al’umma mai kama da mu’ujiza.

Bayanai Ga Maƙwabtan Kudancin Iran

A wannan lokaci ina cewa ga maƙwabtan kudancin Iran: kuna ganin wani abin al’ajabi. Ku gani da kyau, ku fahimta da kyau, kuma ku tsaya a inda ya dace. Kada ku yarda da alkawuran ƙarya na masu mugunta. Har yanzu muna jiran martani mai dacewa daga gare ku domin mu nuna muku ’yan’uwantaka da alheri. Wannan ba zai yiwu ba sai kun nisanta kanku daga masu girman kai da ba sa rasa wata dama wajen wulakanta ku da cin moriyarku.

Kowa ya sani cewa, da izinin Allah, ba za mu bar masu laifi da suka kai hari kan ƙasarmu ba. Za mu nemi diyya ga dukkan asarar da aka yi da kuma jinin shahidai da diyya ga waɗanda suka ji rauni a wannan yaƙi. Haka kuma za mu shigar da gudanar da Mashigar Hormuz cikin wani sabon mataki.

Ba mu nemi yaƙi ba, kuma ba mu son yaƙi; amma ba za mu taɓa barin haƙƙinmu na gaskiya ba. A wannan lamari muna kallon dukkan ƙungiyoyin gwagwarmayar a matsayin abu guda.

Shawarwari Ga Al’ummar Ƙasa

A wannan lokaci, har sai mun kai ga nasara ga abin da ya dace da mu:

Na farko, dukkan jama’a su yi ƙoƙari su kula da juna domin rage matsin lamba da ƙarancin abubuwan da yake faruwa a kowane yaƙi kan sassa daban‑daban na al’umma. Duk da haka, waɗannan ƙarance‑karance an sarrafa su sosai ta hanyar ƙoƙarin gwamnati da sauran cibiyoyi.

Na biyu, dole ne mu kula da kunnuwanmu—waɗanda su ne tagar zuciya da kwakwalwa—daga kafofin watsa labarai da maƙiya ke tallafawa ko waɗanda suke tare da su. Wadannan kafofin ba su da niyyar alheri ga Iran, kuma hakan ya tabbata sau da yawa. Don haka ko dai mu guje musu gaba ɗaya, ko kuma mu kalli duk abin da suke faɗa da babban shakku.

Na uku, duk da cewa lokacin makokin hukuma ya ƙare, al’ummar ƙasa za su ci gaba da riƙe azamar ɗaukar fansa ga jinin jagoranmu shahidi da dukkan shahidan Kallafaffun yaƙe‑yaƙe na biyu da na uku.

A ƙarshe ina miƙa saƙo ga Maigirmanmu Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa): muna tsaye tare da imani ga Allah da kuma tawassuli ga Imamai tsarkaka, muna bin tafarkin jagoranmu shahidi a ƙarƙashin tutarku, muna fuskantar rundunar kafirci da girman kai. Mun sadaukar da shahidai masu daraja daga sassa daban‑daban na al’umma domin ɗaukakar ƙasa da Musulunci da juyin juya halin Musulunci. Yanzu muna fatan addu’arku ta musamman domin samun cikakkiyar nasara a kan maƙiya—ko a tattaunawa ko a fagen yaƙi—kuma muna fatan nan ba da jimawa ba mu da maƙiyanmu za mu ga tasirin wannan mu’ujiza.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei 

20 ga Farvardin, 1405 (09 ga Afrilu, 2026)

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha